1. Kada ka raina iyayenka. Ba za su dawwama ba, ka kula da su matuƙa.
2. Idan ka gyara kanka, kamar ka gyara iyalinka. Idan ka gyara iyalinka, kamar ka gyara al’umma ne, idan ka gyara iyalinsa kai ma ka gyara ni ma na gyara sai al'umma ta gyaru.
Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint
3. Namijin da ya iya fin ƙarfin sha’awarsa yana da cikakken iko kan rayuwarsa.
4. Kunya ta ɗan lokaci ce, amma nadama tana dawwama. Ka fi son fuskantar kunya da wuri a kan ka yi nadama daga baya. Ka yi aiki tuƙuru kada ka ji junyar wulaƙancin jama'a kan sana'arka.
5. Namiji mara manufa yana rayuwa ne kawai don shagaltuwa da abubuwan banza. Kamar zuwa fati, shaye-shaye da neman mata.
6. Ka guji mutanen da ke ƙin jinsin da suka saɓa da nasu; suna da matsala a zukatansu.
7. Ka saurari tsofaffin da suke farin ciki, sun san abin da suka gani a rayuwa.
8. Ɗa’a (hazaƙa) ta fi ƙwazo (motsi zuciya). Ka dinga yin abin da ya dace, koda ba ka jin daɗin aikata shi a ranka.
9. Idan kana jin buƙatar burge kowa, to kai bawa ne gare su.
Duk lokacin da kake son burge mutane za ka zama kamar bawansu . Duk abin da suke so shi za ka aikata ko ba daidai ba ne. Hakan ya sa malamai suka zama karnukan 'yan siyasa.
10. Mafi yawancin baƙin ciki a cikin maza na faruwa ne sakamakon rashin manufa a rayuwa.
Kaso 90 na maza suna faɗawa wahala ne da ƙunci da talauci saboda rashin manufa da gina kasuwanci ko aiki tun suna ƙananu.
11. Idan namiji yana rashin kunya ga uwarsa, kada ki amince da sh, ba zai girmama ki ba.
12. Namijin da ya saba da jin daɗi mara amfani yana lalacewa. Dole ka saba da wahala don ka bunƙasa.
13. Halayen mace suna ƙarfafa namiji, haka nan kuma halayen namiji suna ƙarfafa mace.
Idan namiji ya samu mace mara manufa sai ta rage tasa manufar da kaso 70 haka idan ya samu mai manufa sai ta cike shi ya zama mai ɗari bisa ɗari.
14. Rayuwa ba za ta sauƙaƙa ba, kai ne kawai za ka ƙara ƙarfi don fuskantar ta.
15. Babu wanda ya taɓa zama babban mutum ta hanyar zama kan kujera yana kallon fina-finai da tsalle tsakanin facebook da tiktok tsawon wuni/yini.
16. Namiji yana samun mafi yawan farin ciki ne lokacin da yake gina abin da zai bari bayan ya tafi.
17. Kada ka saurari marasa fata da ke cewa rayuwa tana muni idan shekaru suka kai 40. Idan ka dage, kana inganta ta fiye da matashin ɗan shekara 20.
18. Kasance namijin da ke da nutsuwa lokacin da kowa ke firgice aka rasa mene ne mafita. Yi ƙoƙari ka nemo mafita.
19. Gwamma ka yi kuskure a kokarinka fiye da ka zauna ba ka yi komai ba.
20. Yin dariya da mai kiba a dakin motsa jiki kamar yin dariya da marasa gida ne don yana neman aiki. Wannan rashin tunani ne.
21. Zama cikin yanayin wajen da yake shiru da shan iska yana rage damuwa fiye da shan magungunan maye da giya.
22. Koyi yadda za ka karɓi suka ba tare da ka fusata ko ka mayar da martani da zafi ba.
23. Daina kallon batsa, za ka ji daɗin rayuwa kuma ka fi zama namiji nagari.
24. Ka nemi abin da kake so ta hanyar aiki da ƙoƙari, kada ka yarda da son cin banza da neman alfarma.
25. Ka tuna cewa wasu maza suna da kirki ba don suna da hali mai kyau ba, sai don sun kasa tsayawa tsayin daka wajen kyautatawa mata har matan ke juya su kuma suke ganin mazajen nasu masu kirki ne.