Ba a yin arziki a sana'oin da ake yi cikin unguwanni sai dai a samu na abinci, don kuwa makusantanka da maƙwabtanka suna ganin ka fara tashi za su yi duk mai yiwuwa wajen durƙusar da kai.
Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint
Babban wanda zai iya ceto ka daga talauci ya saka a harkar arziki sam ba shi da alaƙa da kai ta jini ma'ana baƙo ne.
Idan ka sa haka a ranka ka huta da zafin aƙida ko tsatstsaran ra'ayi.
Gajeriyar mace baƙa mai ƙarancin kyawu ta fi kowacce mace biyayyar aure da kaifin hankali wajen zamantakewa da bayar da shawarwari masu amfani da tallafar miji.
Babban maƙiyinka shi ne na kusa da kai.
Kyakkyawar mace doguwa fara ta fi daɗin zaman aure idan kana da dukiya ko kuma kana yawan zuwa taron manyan masu kuɗi da matarka.
Ko ba ka so baban matarka ya fi wasu daga cikin ƙannenka da yayyenka son ganin ka ci gaba a rayuwa.
Bayan mutuwarka matarka sai ta fi wahala da 'ya'yanka akan mahaifiyarka.
Ƙanwarka mace ta fi ƙaunarka akan yayarka mace, kuma ta fi ƙaunarka akan 'yan uwanka maza.
Ƙanwar matarka ta fi rainaka akan ƙannen matarka maza da yayyenta maza.
Jarin farko da aka buɗe kasuwanci da shi indai ba ka koyi kasuwancin tun daga tushe ba ko ka yi zaman yarinta a shagon wani ba, ka ɗauka kawai gidan marayu ka buɗe ba shago ba don jarin sai ya zurare kamar fashashshen kwano.
Ka girmama ra'ayin kowa hatta baƙo ba mamaki mafitarka a rayuwa tana tattare da shi.