Barka Da Shan Ruwa sarauniyata wadda na sadaukar ma da zuciyata. Shiga ki zauna kin zama sarauniya ta musamman a cikin ta, me kike da buƙata a kawo miki ki yi buɗe baki da shi?
Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR
Da Sunan Allah Maɗaukakin Sarkin da ya tsara suffar halittarki cikin daidaituwar kyawun da ke burge dukkan idanuwan da su kai tozali da kyakkyawar fuskarki.
Yau Azumin mu 15 cif shiyasa na dawo gare ki, ba zan gajiya ba tare da jinjina da gaisuwar aminci mai cike da tarin so da ƙauna zuwa gare ki.
Sannunki fa 'yar gaban goshin zuciyata na yi jinjina kuma na gaisheki. Burina ki zamto cikin farin ciki da tarin annashuwa, a daidai lokacin da kike buɗe baki hakan shi ne cikar burina.
Farin ciki abun so ne daga kowace irin nau'in zuciya shiyasa tawa ta kasance cikin shauƙi da annuri kasancewar na samu farin cikin raina.
Na koyi darasin ƙauna kasantuwar na kwana cikin inuwar zuciyar da ta san yadda ake so da tarairayar zuciyar wanda take so.
Kuma da ke zan rayu komai tsananin juyin yanayi muna tare da'iman.
Kowane matsayi, kin cika shi wajen zama sarauniyar mata a cikin zuciyata, da ke zan yi rayuwata.