Wednesday, 26 March 2025

Ƙarya 7 Da Babu Laifi Idan Ku Yi Su

Tura Wannan Zuwa Ga

 1. Shi ne ƙarya da mutum zai da nufin yin wasa, wanda kowa zai iya hanzarin fahimtar cewa wasa mutum yake yi.


Ƙarya 7 Da Babu Laifi Idan Ku Yi Su
Hoto: Minerva Studio/Dreams time

MarubuciTaska


2. Ƙarya da ake yi da nufin wasan kwaikwayo. Kamar wane ya fito shi ne mijin wance, ko matar gwamna ko shugaban ɓarayi da sauransu.


Ana yi ne ta yadda kowa ya san wasan kwaikwayo ne, ba gaskiya ba ne.


3. Ƙarya da mutum zai yi don ƙoƙarin samar da gyara.


Kamar mutum ya je wajen matar da suka rabu da mijinta ya ce mata wallahi ya ga mijinta cikin damuwa da nadama, sai ya garzaya wajen mijin ya ce masa wallahi matarsa tana cikin matuƙar damuwa da nadama.


Wanda manufar hakan shi ne: don ya shiryasu


4. Ƙarya don mutum ya kare kansa ko waninsa daga azzalumai. 


Kamar ɓarayi ko 'yan fashi su tambayi wani: shin nan ne gidan alhaji wane? Sai ya ce: a'a ba nan ba ne.


5. Ƙarya don mutum ya yabi wani ko ya yabi kansa, da sharaɗin babu wanda zai cutu daga wannan ƙaryar.


Kamar yadda masoya suke yi wa kansu ƙarairayi.


Ko kamar mutum ya ce: wane bijimi ne toron giwa, an buga da shi an bar shi, mahassadansa fadawa ne, wane ya fi ƙarfin kowa, ko ya fi kowa hankali, ko ilimi ko sanin ya kamata. 


Kamar ya ce wallahi kaf majalisar dattawa babu wanda ya kai wane haƙuri da zurfin tunani.


6. Ƙarya daga mashaya (tsatso) 

Kamar mutum a tambaye shi ƙarfe nawa ne? Nan take sai ya duba agogo ya ce ƙarfe kaza ne, ashe agogon ba ya tafiya daidai. 


Ko wacce ta fi shahara: ita ce wacce kowa yake yawan yi.


Kamar wane ya ce wallahi duk mai aƙida kaza, a cikin ɓata yake, ko sai ya shiga wuta idan ya mutu.


Sakamakon haka shi ma ya karanto à fahimtar wani malami ko marubuci. 


Ko mafi yawan abin da muke gani a shafukan sada zumunta mu zata gaskiya ce zalla sai mu ma mu yaɗa ta gaba.


Misali a addinance: shi ne Yahudawa suna iitiƙadi cewa lallai Allah yana son su kuma ya fifita su sama da dukkan halittu. 


Musulmai ma suna da irin nasu fahimtar makamanciyar haka.


7. Ƙarya da mutane ke yi don su kori mutum ba tare da sun sa ya ji damuwa ba.


Kamar mutum ya ce don Allah wane zan samu canjin kuɗi kaza? Sai ka ce ai kuwa babu canji, alhalin akwai, amma kana nufin kai ba ka da wanda za ka ba shi ne. 


Ko mai roƙon kuɗi sai ka ce masa ba ka da kuɗi.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user