Tuesday, 4 March 2025

Kyawawan Gajerun Sakonnin Barka Da Shan Ruwa Ga Budurwa

Tura Wannan Zuwa Ga

Yau ce ranar azumin farko a cikinta ne nake fara ba ki saƙon farko wanda a farkon ranar haɗuwarmu zuciyata ta tanaje shi musamman domin ki. Manyan dalilan da suke ƙara saukar da ni'imar sanyin son ki a raina, sun samo alaƙa ne da irin suffatuwarki cikin sufar da ba zan iya misaltawa kowa ba.


Kyawawan Gajerun Sakonnin Barka Da Shan Ruwa Ga Budurwa
Hoto: Freepik

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR


Farkon buƙatar zuciya ita ce ta fara sallama a gare ki cikin farkon rubutuna wanda nake farawa da saƙon da ke nuna girman matsayin muƙaminki a guna.


Buɗe min zuciyarki domin na shigar da saƙon zuciyata wanda yake ƙara danƙon zumuncin da ke a tsakanin junanmu.


Ke kamar ɗanyen farin zinare kike da zarar na kusanto inda kike sai na ji tamkar na zama wani sabon Basarake, a yayinda hasken haƙoranki yake ƙara ni'imtar da zuciyata cikin ni'imar son ki da ƙaunarki.


Sallama a gare ki yake mai martabar girman matsayin muƙamin shiga cikin ƙololuwar fadar zuciyata wanda babu abin da ta sani face son ki da ƙaunarki.


Matsayinki na daban ne a cikin raina. Na yi niyyar hidimtawa soyayyarki dan haka babu gudu kuma babu ja da baya.


Da'iman abadan da ke na yi alƙawarin ƙarasa dukkan rayuwata. Idan ina tare da ke ni ban gano ranar da akasin farin ciki zai riske ni ba.


Haɗuwata da ke shi ne shaidar da ke nuna cewa tabbas na yi bankwana da dukkan wata damuwata. Dan haka nake ƙara shigar da ke a cikin tunanin ruhina.


Aminci a gare ki tare da saƙon sallamar so da ƙauna yake abun tattalin so da ƙaunar da ta kewaye dukkan ruhina a koyaushe.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user