Thursday, 13 March 2025

Muhimman Abubuwa Kan Maza Da Mata

Tura Wannan Zuwa Ga

Mata suna zina ne da wanda suka yi ra'ayi. Yayin da maza kuma ke yi da duk wadda ta ba su dama.


Muhimman Abubuwa Kan Maza Da Mata
Hoto: God design path

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Don haka idan aka aikata zina mace ita ce mai kaso 90 wajen ba da gudummuwa.


Maza na auren macen da suka ga alamun za su iya juyawa ne kuma take nuna musu tausayi tun daga waje shiyasa za ka ga namiji ya shekara biyar yana soyayya da mace amma ya ƙi aurenta rana ɗaya kuma ya haɗu da wata daban cikin wata shida ya aure ta ya ƙyale waccan.


Kaso 90 na matan zamani suna auren wanda ya shirya ne zai yi auren ba ɗan soyayya gwanin iya kalamai da nuna musu soyayya ba amma ba shi da manufa.


Kaso 99 na maza ba su damu da kwalliyar zamani da mata ke yi ba wadda suke mulka kwalliya a fuska, sannan maza ba sa bambance tsadar tufafin da mata suka saka sun fi ganewa idan kayan ya yi musu kyau.


Macen da ta sa jan mayafi ta fi ɗaukar hankali akan wadda ta saka wata kala ba ja ba.


Matan da suka haura shekara 30 babu aure sukan yi fama da lalurar baƙin ciki (Depression). Shekararsu ta farko bayan aure ya kan warke.


Kaso 90 na maza 'yan shekara 25 zuwa sama wanda ba su da aure suna aikata istimna'i (Mastubartion).


Auren mummuna da mai tsakatsakin kyau ya fi na kyakkyawar mace ƙarko.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user