Thursday, 6 March 2025

Takaitattun Sakonnin Barka Da Shan Ruwa Ga Masoya

Tura Wannan Zuwa Ga

Wash yau kam na ji azumi, tabbas ibadar Allah daɗi gareta, Allah dan isar ikon tsarkin mulkin ka Allah, ka karɓi ibadun mu. Barka da shan ruwa shalele.


Taƙaitattun Sakonnin Barka Da Shan Ruwa Ga Masoya
Hoto: Envato

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR


Jijiyoyin da suke kawo jini a cikin jikina suna gaisuwar aminci a gare ki.


Kalaman da ke fitowa daga bakina sun kasance mallakinki ne ke kaɗai.


Kuma ba zan so ki ba wa kowa ba.


Na so ki ba zan so 'yar gidan kowa ba.


Ƙaunarki kaɗai ita ce na zaɓa har na yi mata babban masauki a cikin fadar zuciyata.


Da farkon farawar ranar da ta fito daga gabas zuwa yamma, tunaninki bai bar zuciyata ta samu sukuni ba.


Murna nake da ganin ki 'yar gata, zo ga wuri zauna, idanuwana su kalli kyawun da ke fita daga gare ki.


Ina son ki, na san ina ran ki kamar yadda ke ma kike raina.


Dan haka ina da ƙwarin gwiwa a kan son da kike a gare ni.


Ina  son ki wannan ita ce kalmar da nake amfani da ita wajen saita zuciyata a daidai lokacin da nake tunaninki.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user