Monday, 17 March 2025

Yarinyar Da Kake Soyayya Da Ita

Tura Wannan Zuwa Ga

Matashi bari na gaya maka gaskiya, yarinyar nan da kuke soyayyar kashe lokaci da ita tana da damar samun ingantacciyar rayuwa fiye da kai, tun wuri ka dawo hayyacinka, kar ka kuskura ka ƙarar da duk ƙuruciyar ka a gina dangantaka da mata.


Yarinyar Da Kake Soyayya Da Ita
Hoto: iStock photo

Marubuci:- Abdullahi Madachi 


Gaskiyar da ba ka sani ba ita ce, 'yammata masu soyayyar kashe lokaci ƙarshe auren maslaha suke yi, duk zaƙin soyayyarku za ta tsere idan ta samu wanda ya fi ka ko wanda ya riga ya shiryawa yin aure wanda suke wa laƙabi da "Ready Made"  Mutumin da ya riga ya gama ɗora rayuwarsa akan "Turba" mai kuɗi da isassun kayan aiki.


Lokacin da za ta ware ta bar ka cikin mummunan talauci da tarin tunani kala-kala kamar kanka ya yi bindiga, lokacin za ka gane asarar da ka yi wajen gina soyayya maimakon gina kasuwanci ko koyon wata sana'ar hannu.


Don haka ba kyautawa ba ne ka ɓata lokacinka, tunaninka, kuɗinka, akan macen da ka san ba ka da tabbacin aurenta kuma ba ka da damar aurenta.


Ita mace ba ta da asara kamar namiji a irin soyayyar nan don kuwa ita lokaci ne kawai take ɓatawa shi kuwa namiji yana rasa abubuwa da yawa, kamar kuɗin da rashin maida hankali wajen neman kuɗin kansa.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user