Zuciyata ce kaɗai za ta iya bayyana zahirin yadda nake ji a kanki. Zan iya zuwa ko'ina ne da ƙafata a cikin duniya, matuƙar hakan zai sanya ki farin ciki. Ina son ki fiye da so. Barka da shan ruwa.
Marubuci: Abba Muhammad Dan Hausa
Baiwa ce ta musamman samun ki a matsayin wadda zuciya ta aminta da ita.
Kasancewar ki a tare da ni, yana ƙara tabbatar da irin yadda albarka ta ke ƙara mamaye cikin rayuwata.
Zan kasance cikin soyayyarki har zuwa ranar fitar numfashina na ƙarshe, duk daɗi duk wuya.
Barka da shan ruwa abar ƙauna, ina fatan ƙishirwa ta tafi, jijiyoyi sun jiƙu lada ya tabbata da yardar Allah. Ki huta lafiya.
Son ki a cikin zuciyata, ya zarce zuma zaƙi, kyawunki ya ɗara na dukkan kyawawan furanni.
Na gode da kasancewarki a cikin rayuwata. Ina son ki, fiye da girman kowace kalma da ta ke iya bayyana so. Fatan kin sha tuwa lafiya?