Suna cewa so ba a iya ganinsa, a na jinsa ne kawai a cikin zuciya, amma ni ina ganin sun yi kuskure, saboda na gan shi kuma ina ganin son da ki ke yi min na gaskiya a cikin ƙwayar idanuwanki, wanda shi ne abu mafi kyau da burgewa da na taɓa gani a duniya. Ina son ki. Ki kwana lafiya.
Marubuci: Abba Muhammad Dan Hausa
Matata, uwar 'ya'yana, farin cikin raina barka da yammaci, duk da kasancewar mun ɗan yi nesa da juna, ina cikin aiki tun bayan fita ta daga gida, amma tunaninki da bege, su ne suke taya ni hira, suke rage min gajiya da kawar da hankalina daga ci da sha na tsawon rana.
Yaya girke-girke da sauran aikin gida? Ki ci gaba da kula min da kanki har zuwa lokacin da zan dawo. Ina nan zuwa gare ki babu jimawa. Ki kasance cikin ƙoshin lafiya. Ina son ki.