Friday, 11 April 2025

Gaskiya 7 Da Babu mai Sanar Da Ku Su

Tura Wannan Zuwa Ga

1. Sauƙin kai ga kowa yana rage maka daraja


Idan kana da sauƙin kai ga mutane, suna kallonka a matsayin wanda bai da wata daraja ta musamman.


Gaskiya 7 Da Babu mai Sanar Da Ku Su
Hoto: Freepik

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Misali, kullum da an neme ka za a same ka kullum kana liƙe da mutane to lallai waɗannan mutane za su rage ganin darajar ka .


2. Mutane ba sa son gaskiya, sai abin da ya dace da ra’ayinsu


Yawancin mutane ba sa son gaskiyar da za ta motsa su ko ta canza tunaninsu, sai dai su ji abin da ya dace da abin da suka riga su gaskata.


Misali, idan wani ya yi imani da cewa duniya tana da siffar leda, ba zai so jin hujjojin da ke nuna akasin hakan ba.


3. Za ka iya ruɗar da kanka idan ka maimaita ƙarya sau da yawa


Idan mutum yana maimaita wani abu, koda ƙarya ce, a hankali zai iya fara gasgata hakan. Misali, idan ka ci gaba da cewa kai ba ka da kyau ko basira, lokaci zai zo da hankalinka zai gasgata hakan, cewa kai mummuna ne ko daƙiƙi ne kai.


4. Shiru a yayin ciniki yana ba da nasara


A duk lokacin da ake ciniki ko tattaunawa mai muhimmanci, wanda ke magana kaɗan shi ke da iko. Wanda yake magana marasa yawa a irin wannan tattaunwa ta ciniki ko yanke shawara maganarsa ita ta fi muhimmanci kuma ta fi cike gurbin da ake buƙata wajen tsayar da matsaya.


5. Mutanen da ke tilasta ka yawan bayanin a kanka suna sarrafa ka ne


Idan wani yana yawan jefa ka cikin halin da za ka riƙa kare kanka da bayanai, yana iya zama yana ƙoƙarin sarrafa tunaninka.


Misali, idan wani yana son ya ja hankalinka zuwa ga laifinka, zai sa ka yawan bayani har sai ka ji kamar kai ne ke da matsala.


6. Jinkiri kafin amsa tambaya na iya nuna ƙarya ce maganar


Idan mutum ya tsaya yana tunani kafin ya ba da amsa ga tambaya mai sauƙi, yana iya nuna yana ƙoƙarin ƙirƙirar amsa maimakon ya faɗi gaskiya. 


Misali, idan ka tambayi wani: "Kana ina jiya da dare?" Sai ya yi jinkiri kafin amsawa, hakan zai iya nuna yana ƙoƙarin tunanin wata ƙarya mai ma’ana da zai ƙirƙira ya gaya maka.


7. Shiru


Idan mutum yana shiru bayan wata magana ko rikici, hakan na sa ɗayan ɓangaren jin damuwa da ƙoƙarin yin sulhu.


Misali: Idan mutum ya ƙi yin magana da kai, za ka iya jin kamar kai ne da laifi, duk da ba haka ba ne.


Me ya kamata a yi da wannan Ilimi?


Waɗannan dabaru na dark psychology ana amfani da su a zamantakewa, kasuwanci, da siyasa.


Fahimtarsu na iya taimaka wa mutum wajen kare kansa daga sarrafawar wasu ko kuma amfani da su a hanyoyin da suka dace.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user