Wednesday, 16 April 2025

Kyawawan Sakonnin Gaisuwar Barka Da Safiya Ga Masoyiya

Tura Wannan Zuwa Ga

Kasancewarki sarauniya mai cikakken iko, na san yanzu haka kina kwance ba ki tashi daga bacci ba, shiyasa na aiko saƙona domin ya zauna a bakin fadarki ya jira lokacin tashinki, sai ya yi gaisuwar aminci a gare ki.


Kyawawan Saƙonnin Gaisuwar Barka Da Safiya Ga Masoyiya
Hoto: Next luxury

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR


Sallamar aminci cikin amintar da ke amintar da ruhin zuciya, gaisuwa nake biyawa zuwa gare ki.


Ina cikin tsakiyar son ki, cikin wata sabuwar duniya ta musamman, mai ɗauke da kayan alatu masu faranta ruhin jikina.


Na koyi darasin ƙauna kasancewar na kwana cikin inuwar zuciyar da ta san yadda ake so da tarairayar zuciyar wanda take so.


Ke nake so kuma zuciyata take yayi. Ya zan yi na iya tsallakewa bayan kin mamaye dukkan jikina?


Kowanne matsayi kin cika shi wajen zama sarauniyar mata a cikin zuciyata, da ke zan yi rayuwata, kuma da ke zan rayu komai tsananin juyin yanayi muna nan tare da'iman.


Ina miƙa saƙon gaisuwa mai ɗauke da fatan amincewar ruhin zuciyarki. Fatana kawai ki ce min kin tashi cikin ƙoshin lafiya.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user